About Us

Dan Lanjeriya gidan jarida ne na yanar gizo wanda ya shahara wajen wallafa gangariyar labaran cikin gida Najeriya, Nijar, Kamaru, Cadi da ma sauran ƙasashen duniya baki daya.

Shafin ya shahara matuƙa wajen kawo labaran duniya, siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, kiwon lafiya, fannin addini, al'adu, kimiya da fasaha, labaran aiyuka, abubuwan almara da ma sauran al'amuran yau-da-kullum.

Har-ila-yau shafin ya kasance zakaran-gwajin-dafi wanda ya ke baiwa marubuta damar fadin ra'ayoyinsu domin sauran al'umma su ji kuma su yi alƙalanci.

Bugu-da-kari shafin Dan Lanjeriya ya na baiwa kowanne marubuci damar yin dogon sharhi akan al'amuran yau-da-kullum da ke faruwa a yankunansu, jihohinsu da ma ƙasarsu.

Babu shakka, muna fata wannan shafi zai bada tashi gudunmawar wajen kawo cigaba a Kasashen Afirka.