Yanzu muka samu labarin rasuwar mahaifiyar jarumin finafinan Hausa, Haruna Talle Mai Fata ɗanuwa ga Hamza Talle Mai Fata.

Haruna, ɗa ga mamaciyar shi ne ya fitar da sanarwar rasuwar mahaifiyar tasu a kafar sada zumunta ta Instagram a wani post da ya yi.

Haruna da Mahaifiyarsa
Haruna da Mahaifiyarsa

Kamar yadda aka bayyana, za a yi jana'izarta a kofar gidanta da ke Mil tara, Karamar Hukumar Ungogo, jihar Kano.

"Innalillahi wa Inna,ilaihirraji'un Allah yayiwa mahaifiyata rasuwa yau za,ayi jana'izarta akofar gidanta dake kano mil Tara.

"Allah yajikanta da Rahama

12/01/2022 " kamar yadda Harunan ya wallafa a Instagram @haruna_talle_maifata

Tuni dai an sallaci mahaifiyar ta jarumi Haruna Talle Mai Fata, sai mu ce Allah ya jikanta ya sa karshen wahalar kenan.

Labari na baya Labari na Gaba