_Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu shi ya bayyana hakan yayin zantawarsa da menama labarai a Gusau.

_Ya kuma bayyana dare a matsayin lokacin da 'yan fashi suka fi amfani da shi wajen tare matafiya da yin garkuwa da su a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bukaci dukkanin direbobi da kuma fasinjojin jihar da su guji yawan tafiye-tafiye cikin dare.

Motar Autan Direbobi, Zazzau
Motar Autan Direbobi, Zazzau

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a ranar 31 ga watan Disamba, 2021.

Mista Shehu ya yi wannan furucin ne bayan jami’an ‘yan sandan jihar sun yi nasarar ceto wasu daliban Islamiyya 21 da wasu ‘yan bindiga suka sace a kauyen Kucheri.

Kazalika ya bayyana dare a matsayin lokacin da ‘yan fashi suka fi amfani da shi wajen tare matafiya tare da yin garkuwa da su a jihar.

“Rundunar tana kira ga jama’a musamman direbobi da fasinjoji da su daina tafiyar dare.”

“Daren dare shine lokacin da ‘yan fashin suka fi amfani da su wajen tare hanyoyi da yin garkuwa da matafiya a jihar.”

Labari na baya Labari na Gaba