Har-ila-yau a daren jiya Litinin din, wasu ‘yan bindiga a kan babura kowannensu dauke da goyon mutum 2, suka kai hari unguwar Gbayi Villa da ke bayan Polytechnic din Kaduna inda suka kashe mutum 1 tare da yin awon gaba da matarsa mai ciki.

'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Sai dai wani shedar gani da ido kuma mazaunin unguwar ya shaida wa manema labarai cewa, wasu ‘yan bindigar da dama sun hade da wadanda suka shiga unguwar a kan baburan.

Kamar yadda jarirdar Vanguard ta ruwaito, mazaunin unguwar ya ce  “Sun shiga cikin unguwar ta gefen kogi suna tafiya suna sanda kamar birrai”

“Lokacin da suka shigo cikin jama’a, mutane sun ranta a na kare amma wani mutum  da ya yi kama da ‘yan banga ya tsaya yana kokarin kiran waya da wani abu kamar oba-oba. ‘Yan bindigar take suka harbi mutumin a ka, ya fadi ya mutu,” inji mazaunin.

Ya kuma yi zargin cewa baya ga matar marigayin da ‘yan bindigar suka dauka, sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna unguwar 10 a wani samame da suka dauki sama da awa daya.

Har yanzu hukumomin tsaron jihar Kaduna basu fitar da sanarwa game da lamarin ba.
Labari na baya Labari na Gaba