'Yan sanda a Birnin Nairobi na kasar Kenya na kan gudanar da bincike kan wani lamari mai sarkakiya.

Inda wani mutum dan shekaru 42 ya mutu a lokacin da yake tsaka da kwasar dadi shi da masoyiyarsa yar shekara 20 a wani masauki a Kawangware.

Ma'aurata
Hoto: Alamy.com

Mutumin mai suna Erastus Madzomba ya sadu da budurwarsa Elgar Namusia mai shekaru 20 makonni biyu da suka wuce.

An kuma samu gawarsa a Gidajen Broadway kusa da Titin Thiong'o.

A cewar wani rahoton 'yan sanda da TV47 Digital ya gani, masoyan sun yi jima'i a gaban mutumin fita hayyacinsa.

'Yan sanda sun kai gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki na birnin suna jiran bayanan mutuwarsa don gudanar da bincike.

Labari na baya Labari na Gaba