Jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Tinubu ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Buhari a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu, 2022.

Tinubu da Buhari
Tinubu da Buhari

Zai nemi tikitin takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC). 

Dan siyasar ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya zama shugaban kasa, inda ya ce in aka yi duba da irin ayyukan ci gaban da ya yi a Legas lokacin da yake gwamna, to yana da karsashin mulkar Najeriya.

Ya ce: “Na amsa da cewa eh. Na sanar da shugaban kasa niyyata amma har yanzu ban sanar da ‘yan Najeriya ba. Har yanzu ina shawara. Kuma ba ni da matsala wajen shawara. Kuma ina kasafta Æ™ayyadaddun mutane nawa zan yi shawara da su.”

“Da sannu za ku ji duk abin da kuke so ku ji dag gareni. Kuma kun sami wannan gaskiyar daga gare ni cewa na sanar da shugaban kasa burina.”

Tinubu ya ce babu abin da zai hana mai rike da sarautar zama sarki sai in kisa ya yi.
Labari na baya Labari na Gaba