Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun lalata wata haramtacciyar kasuwa da 'yan ta'adda suka yi a kauyen Gallo Malawari da ke jihar Borno.

Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce an kashe ‘yan ta’adda uku a yayin farmakin.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

A cewar sanarwar: “Rundunar sojojin Najeriya, a yayin da suke kara kaimi wajen ganin sun dakile ‘yan ta’adda a jihar Borno, sun samu gagarumar nasara a kan ‘yan ta’adda a Damask a ranar 7 ga watan Janairu, 2022.

“An kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu, suka mika wuya bayan sun ga ba mafita.

Ya kara da cewa“Rundunar sojojin, yayin da suke gudanar da aikin share fage mai suna Operation DOMINANCE I, sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, babbar mota, babura biyu, magazine hudu da harsashi 7.62mm, da dai sauransu.”

Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ne ya ruwaito labarin tare da sahihantar da shi.
Labari na baya Labari na Gaba