Jam’iyyar PDP ta yi ikirarin cewa ita fa ba ta bai wa wani daga cikin ‘yan Arewa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa ba a zabe mai zuwa na 2023.

Zanga-zangar PDP
Zanga-zangar PDP

Hakan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya ce jam’iyyar ta ware tikitin takarar shugaban kasa a 2023 zuwa Arewa.

Aliyu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a lokacin da mambobin kungiyar goyon bayan Atiku suka kai masa ziyara a Minna, ya ce jam’iyyar PDP ta fidda dan takarar shugaban kasa daga Arewa.

Ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar mayar da shugabancin kasar zuwa Arewa ne biyo bayan bukatar da wasu ‘yan Najeriya suka yi.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar mai taken, “Ba mu sanya tikitin takarar shugaban kasa ba,” ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, PDP ta bayyana kalaman Aliyu a matsayin yaudara.

Haka kuma ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da kalaman na Aliyu, suna masu cewa ba ta wakilci jam’iyyar PDP kan batun.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hankalin jam’iyyar PDP ya karkata kan kalamai da jita-jita daga wasu mutane da ke ikirarin cewa jam’iyyar mu ta ware tikitin takarar shugaban kasa a wani yanki na kasar nan. Wannan lamarin don kawo rudu aka yada shi domin ba ya wakiltar matsayin jam’iyyarmu.

“Don kaucewa shakku, jam’iyyar PDP ta fito karara ba tare da wata shakka ba ta bayyana cewa ba ta ware tikitin takarar shugaban kasa a wani bangare na kasar nan ba. Don haka jam’iyyar PDP ta bukaci ‘yan Najeriya, jiga-jigan mambobi da magoya bayan PDP da su yi watsi da ikirarin shiyya-shiyya marasa tushe da ake yi. Jam’iyyarmu kuma ta gargadi masu yin ikirarin cewa su daina katsalandan.”
Labari na baya Labari na Gaba