Mutuwar wani dama masu iya ka magana sun ce tashin wani, yayin da matukan baburan ‘dan sahu suka tafi yajin aiki a jihar Kano sai kasuwar masu motoci yar kurkura ta bude.

Yayin da wasu da dama ke yin tattaki a kafofinsu domin zuwa inda za su a kwaryar birnin Kano yau litinin, wasu kuwa sun yi amfani da damar da rabbani ya basu.


Lamarin hawa mota ‘yar kurkura yayin yajin aikin masu adaidaita sahu sai ya zamto bakon lamari wanda mutanen jihar Kano basu saba gani ba.

Motoci ‘yan kurkura aka hango makil da mutane ana jigilarsu zuwa sassan birnin Kano, wadda da akwai babur mai kafa uku da ba su hau ba.

Dama dai tuni matuƙa baburan adaidaita sahun suka yi barazanar tsunduma yajin aikin, don nuna damuwar su kan yadda hukumar KAROTA ta tilasta musu sauya lamba da kuma takardun lasisin tuƙi.

Wanda hakan ya jefa zullumi da fargaba a zuƙatan al’umma, kasancewa direbobin sun taɓa tafiya yajin aiki a shekarar 2021
Labari na baya Labari na Gaba