Sanin gaibu kam wannan sai lillahi haka kuma sanin abinda zai faru gobe wannan shi ma yana ga mai duka.

Buhari da Ibrahim Yala
Buhari da Ibrahim Yala

Fitaccen tsohon mawakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato Ibrahim Yala Hayin Banki wanda ya wake buhari lokacin yana jam’iyyar CPC ya fito karara ya nemi afuwar kafinanin ‘yan Najeriya.

Mawakin wanda ya rera wakar  Bakandamiyar Buhari mai taken "Yau Najeriya Riko Sai Mai Gaskiya" ya nemi ‘yan Najeriya da su yafe masa kan angaza mai kan tururuwar da yayi musu ta hanyar koda Buhari.

Ya kuma sha alwashin yin sabbin wakoki wadanda a cikinsu zai warware dukkanin kalamai da kuma baitukan da ya yi wa Buharin. Kamar yadda shafin HausaLoaded ya ruwaito.

Mawakin ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo day a wallafa a kafar Instagram da Tiktok.

Kazalika ya kuma fara rera wata sabuwar waka ta bai wa ‘yan Najeriya hakuri domin su gafarceshi kan kuskuren da yayi a baya na wake Buhari.

Idan baku manta ba, wakar Yau Najeriya na da baituka masu tarin yawa, kamar irinsu “Baba in da rai da rabo mai gida, zai gyara kasarmu a kau da mazambata yau Najeriya tana gaskiya”.

Wakar kam ta yi dadi a wancan karon, to amma fa da Buharin ya dare Mulki sai jikin talakawa ya fadi masu yadda basu yi zato ba.

Labari na baya Labari na Gaba