Komai kam da lokacinsa kuma da ma shi aure ai nufi ne na Allah, kuma tamkar zuwa Hajji ne wato ko da kudinka sai lokaci ya yi kuma sai da rabonka.

Shahararren mai iya barbade fuskar ‘yam mata da hodar nan, wato mai yi wa jaruman Kannywood kwalliya, Mansur Make-up zai angwance tare da amaryarsa.

Za a daura auren nasa ne a ranar Asabar, 8 ga watan Janairun shekarar 2022.

Kalli kyawawan hotunan Mansur Make-up tare da amaryarsa, wadda za su amarce da angwance ranar Asabar.
Sai dai kamar yadda aka fitar a jikin kalantar gayyatar zyuwa wurin daurin auren, da an so yin auren a cikin watan Disamba, 2021 amma wani tsaiko ya sa aka daga sai Janairu.

Mai kwalliyar ya fitar da wannan sanarwar ne a shafinsa na Instagram, yayin da al'umma da dama suka sanyawa auren nasa albarka tun kafin a daura shi.
Labari na baya Labari na Gaba