Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta gudanar da allurar rigakafin sabuwar cutar polio mai nauyin cVDPV2 gida-gida, a kaf fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Rigakafin Polio
Rigakafin Polio

Kwamishinan lafiyar na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayana hakan a wani taroon manema labarai a Kano ranar juma’a.

Mista Tsanyawa ya tabbatar da cewa an samu bullar cutar ta cVDPV2 a cikin jihohi kusan 13 na Tarayyar kasar ciki har da Kano kuma hakan na bukatar daukar matakan dakile barkewar cutar.

"Kawo yanzu Kano ta sami rahoton bullar cutar guda 106 na cVDPV2 a fadin kananan hukumomi 25 a shekarar da ta gabata, 2021.

"An gudanar da ayyukan mayar da martani (OBR) a cikin 2021 a duk kananan hukumomin da abin ya shafa daidai da umarnin kasar Najeriya da kuma ka’idoji dagab Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko," in ji shi.

Mista Tsanyawa ya bayyana cewa, ana gudanar da wani gagarumin gangamin yaki da cutar mai suna OBRI a fadin tarayyar kasar nan domin yi wa duk yaran da suka cancanta allurar rigakafin cutar. 

A cewa kamishinan, atisayen na gida-gida zai kasance cikin makon duba lafiyar jarirari wanda zai fara daga ranar 9 zuwa 13 ga Janairu.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar da yi wa duk yaran da suka cancan rigakafin gaba daya domin dakile yaduwar cutar Poliovirus da ke yaduwa a jihar. 

NAN
Labari na baya Labari na Gaba