Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya hada kai da sauran hukumomin tsaro, kansiloli da sarakunan gargajiya domin kamo wadanda ke da hannun wajen hada-hadar ‘danyen mai ba bisa ka’ida ba domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Gwamna Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike

Gwamnan ya zargi masu satar ‘danyen mai ba bisa ka’ida ba da laifin janyo gurbatar muhalli da ke barazana ga lafiyar mazauna jihar.

Ya ba da umarnin yin liyafar cin abincin dare da karrama rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, wanda aka gudanar a babban ofishin ‘yan sanda da ke Fatakwal ranar Juma’a. 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri ya raba wa manema labarai. 

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Cif Emeka Woke, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar shawo kan masu satar danyen mai da maganinsu baki daya. 

Wike ya bayyana cewa gwamnati a shirye ta ke ta baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro duk abin da ake bukata domin wargazawa tare da kawo karshen ayyukan satar mai a matatu a jihar Ribas.

Labari na baya Labari na Gaba