Gwamnatin jihar Filato, Simon Lalong ya yi Allah wadai da kisan mutum uku da wasu ‘yan bindiga suka yi ranar lahadi a garin Rafin Bauna, Karamar Hukumar Bassa da ke jihar.

Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong

Allah wadan da gwamnan ya yi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na sa, Dakta Makut Maham ya fitar ranar Litinin a Jos.

Mista Lalong ya ce harin wani mummunan yunkuri ne na makiya zaman lafiya domin sfara sabuwar shekara da tashin hankali.

Ya kuma yi gargadi cewa gwamnati ba za ta lamunci irin wannan yunkuri ba kuma za ta maida raddi da duk irin kayan aikin da take da shi.

Karanta kuma: 'Yan bindiga sun kashe mutum 7 sun jikkata da dama a kasuwar Jihar Filato

Gwamnan ya bayyana cewa maharani sun yi wa matafiyan kwanton bauna ne tare da kashe su a kan hanyar Dutsen Kura zuwa Rafin Bauna.

Ya kuma umurci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gudanar da cikakken bincike a kan lamarin domin tabbatar da cewa an kama wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Mista Lalong ya ce gwamnati ta dukufa wajen tunkarar masu aikata laifuka da muggan ayyukansu, ya kuma gargadi masu aikata laifuka da suka hada da masu garkuwa da mutane da su fice daga Filato domin duk wanda aka kama da laifin satar mutane zai fuskanci hukuncin kisa.

Ya jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da ba su tabbacin yin adalci, ya kuma kara da cewa gwamnati za ta kara yaki da miyagun laifuka musamman garkuwa da mutane da ya zama barazana ga zaman lafiya da tsaro a jihar.

Labari na baya Labari na Gaba