Hukumar kula da zaman lafiya ta duniya (GPI) a mujallarta bugu na 15 ta bayyana Ghana a matsayin kasa mafi zaman lafiya a yammacin Afirka

Shugaban Kasar Ghana
Shugaban Kasar Ghana

 Hukumar ta GPI wadda ta sanya kasashe 163 bisa jerin matakin zaman lafiya, ta sanya Ghana a matsayin kasa ta farko a yammacin Afirka da ke zaune cikin lafiya.

Kazalika kasar ta Ghana ta zamto ta biyu a Afirka, kuma ta 38 a duniya a jerin kasashe masu zaman lafiya.

Ita dai hukumar GPI ita ce babbar ma'aunar zaman lafiyan kasashe a duniya kuma cibiyar Tattalin Arziki da Zaman Lafiya (IEP) ce ta samar da ita.

A cewar GPI, rahoton ya gabatar da mafi kyawun bincike da aka yi amfani da shi a yau game da yanayin zaman lafiya, darajar tattalin arziki, da kuma yadda za a bunkasa zaman lafiyar al'ummomi.

Haka kuma a cikin rahoton na GPI aka bayyanar Mauritius a matsayin kasa mafi zaman lafiya a Afirka, yayin da Botswana ta zo ta uku a Afirka.  

Iceland ta rike matsayinta a matsayin kasa mafi zaman lafiya a duniya, matsayin da kasar ke rike da shi tun 2008.

 Da yake mayar da martani ga rahoton, shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bukaci 'yan Ghana da su cigaba da wanzar da zaman lafiya a kasar.

 "Mu ci gaba da kiyaye zaman lafiyar da muke da shi a Ghana," in ji shi a shafin Twitter.

Labari na baya Labari na Gaba