Firayim Ministan Sudan ta Kudu Abdalla Hamdok ya yi murabus bayan wata zanga-zanga da aka yi ta yini guda da ta girgiza babban birnin kasar Khartoum.

Abdalla Hamdok
Abdalla Hamdok

Masu zanga-zangar na kuwwar "iko ga mutane" sun yin kira da a dawo da cikakken mulkin farar hula ba mulkin kashi mu raba da sojoji ba.Dubban mutane sun yi zanga-zangar adawa da yarjejeniyar da Firaminstan ya rattaɓawa hannu kwanan nan ta "raba mulki da sojoji", wadanda suka yi juyin mulki a watan Oktoba.

Amma sojojin sun yi amfani da karfin tuwo wajen mayar da martani kuma hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

Matakin da Mista Hamdok ya dauka na yin murabus ya bai wa sojoji cikakken ikon gudanar da mulkin kasar Sudan.

Tashin hankalin jama'a a shekarar 2019 shi ya haifar da kifar da gwamnatin Tsohon shugaban Suda ta Kudu Omar al-Bashir a 2019.

Kawo yanzu al'ummar Sudan ta Kudi na yunkurin ganin an dawo da mulkin dimokuradiyya na.

 A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, Mista Hamdok ya ce kasar ta kasance a "cikin haɗari wanda ke barazana ga yiwuwar cigaba da dorewarta baki daya".

Labari na baya Labari na Gaba