Sojojin Najeriya sun dakile wani hari tare da kashe 'yan ta'adda biyar a Kwanan Bataro da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, kamar yadda kwamishinan tsaro  harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya bayyana.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

“A bisa ga bayanan da aka bayar, sojojin da ke aikin sintiri a karamar hukumar Giwa sun samu sahihan bayanan sirri na motsin ‘yan ta’adda a garin Fatika,” in ji Mista Aruwan.

“Sannan sojojin sun yi tattaki zuwa Marke da Ruheya domin mayar da martani.

 “An ga ’yan bindgar kuma sun yi yunkurin tserewa sojojin da suka rufo su. Sai dai sojojin sun dakile hanyar tserewa a Kwanan Bataro, inda suka yi musu luguden wuta, inda aka kashe biyar daga cikin 'yan ta'addar. Sojojin sun koma sansaninsu ne bayan sun tabbatar da share bata garin daga yankin.”
 
Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana jin dadinsa da yadda aka samu rahoton aikin, sannan ya yabawa rundunar bisa yadda suka yi taka-tsantsan da kuma maida martani ga bayanan sirri da suka samu.

Ya kuma kara musu kwarin guiwa da su ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a yankin.

Jami’an tsaro na ci gaba da sa ido da kuma sintiri a yankin baki daya.
Labari na baya Labari na Gaba