Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada sabon shugaban bankin bada lamuni (a turance Mortagage Bank) na Najeriya.

Shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa Buhari

Shugaban ya amince da nadin Ayodeji Gbeleyi a matsayin shugaban kamitin gudanarwa na bankin bada lamuni na Najeriya (FMBN).

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina a ranar Juma’a a babban birnin tarayya Abuja.

Femi Adesina ya ce, "Gbeyi kwararren akawunta ne, mataimaki a cibiyar haraji ta Chartered Institute of Taxation kuma sanannen masanin harkokin kudi ne wanda ya taba rike mukamin kwamishinan kudi a jihar Legas.”

Mista Gbeleyi, wanda kuma kwararre ne a fannin sufurin jirage masa, ya maye gurbin Cif Adewale Adeeyo, wanda ya rasu kwanan nan. 

NAN
Labari na baya Labari na Gaba