Tsegungumi sun karade shafukan sada zumunta akan haduwar Mansurah Isah da kuma tsohon mijinta Sani Musa Danja a cikin wani sabon shirin fim mai suna “Hanan”.

Mansurah Isah da Sani Danja
Mansurah Isah da Sani Danja

Mutane da dama sakamakon ganin tsoffin ma’auratan cikin wani sabon shirin tare, sun zargi ko akwai wata a kasa?

Domin rarrabe tsakanin Zare da kuma Abawa ina da yakinin dole sai an zo sashen daga bakin mai ita, domin kuwa tafi dadi.

Tuni dai jaridar Aminiya ta dasa wa wannan tsegumi da ke yawon tsi-tsi tsi-tsi a kafafn sada zumunta aya.

Inda ta yi wata hira ta musamman da tsohuwar matar Sani Danja, wato Mansurah Isah.

To sai dai a cikin mun jiyo Mansurah Isah na ikirarin ita fa ba wanda ya isa ya rabata da tsohon mijinta Sani Danja.

Ta kuma ce yadda ta ga rana haka ta ga dare a jajibirin haska ‘Fanan’ a sinima.

To ko me ya sanya jarumar finafinan hausar yin wannan ikirari? Kokarta kallon cikakkiyar hirar domin sanin ainihin wannan tambaya.

Kalli cikakkiyar hirar:

Labari na baya Labari na Gaba