Shugaban karamar hukumar Akwanga ajihar Nasarawa, Emmanuel Leweh ya rasu.

A cewar majiyoyi, an kwantar da marigayi Leweh ne bayan da ya fadi a ofishinsa da ke sakatariyar Akwanga a ranar Litinin.

Emmanuel Joseph Leweh
Emmanuel Joseph Leweh

Leweh, wanda bai wuce watanni uku a kan karagar mulki ba, ya rasu ne a yau (Alhamis) a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja inda yake jinya tun bayan da ya fadi.

Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa, Samuel Tsebe, ya sanar da rasuwarsa ga sauran‘yan majalisar a daren Alhanis.

Ya ce, “Na rasa babban yayana, Honarabul Emmanuel Joseph Leweh, shugaban  karamar hukumar Akwanga a yammacin yau bayan gajeriyar rashin lafiya.”

Labari na baya Labari na Gaba