Kyaftin din Najeriya, Ahmed Musa ya bayyana cewa gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2021 ka iya zama wasansa na karshe da zai wakilci Najeriya a wasannin nahiyar Afirka.

Ahmed Musa
Kyaftin din Najeriya Ahmed Musa

Tauraron dan wasan na Fatih Karagumruk yana cikin 'yan wasa 27 a tawagar Austin Eguavoen da ke Garoua, kuma yana cikin ‘yan wasanda za su fafata a gasar cin kofin Afrika karo na uku ranar Talata.

Musa yana cikin tawagar Stephen Keshi wadda ta lashe gasar a Afrika ta Kudu a shekarar 2013, sannan kuma ya taimakawa tawagar Gernot Rohr lashe tagulla a gasar da aka gudanar 2019 a Masar.

Gabanin wasan farko na rukunin D da Super Eagles za ta yi da Masar a filin wasa na Roumde Adjia, kyaftin din mai shekaru 29 ya bayyana cewa ya tattauna da sauran 'yan wasan kan irin kyautar da za su ba shi.

“Ina ganin wannan zai iya zama gasar cin kofin Afrika ta karshe da zan bugawa Najeriya,"”in ji Musa a wani taron manema labarai.

“Na bayyana mahimmancin wannan gasa ta Afcon ga takwarorina, kuma na fada musu kyautar da za su iya ba ni ita ce lashe wannan gasar, kuma sun gaya mini cewa za su yi.

 “Gasar farko da na yi da Najeriya ita ce gasar cin kofin Afrika ta 2013 da aka yi a Afirka ta Kudu, inda muka yi nasarar lashe kofin, kuma karo na biyu a Masar ne muka zo na uku.
 
“Duk lokacin da aka kira ni don yi wa kasa hidima ta kasa-da-kasa, koyaushe zan amsa kira.”
Labari na baya Labari na Gaba