Wata babbar kotun Ado Ekiti ta yanke wa wani matashi mai shekaru 24 mai suna Ebenezer Olorunkele hukuncin kisa ta hanyar rataya bida samunsa da laifin kashe ‘dan uwansa.

Kisa ta hanyar rataya
Kisa ta hanyar rataya

Kotun ta zartar da hukuncin ne bayan saurayon karar a zaman karshe wanda aka yi a ranar Litinin.

Mai shari’a Bamidele ya ce masu gabatar da kara sun kawo hujjoji da shaidojin da suka tabbatar da Olorunkele Ebenezer da ake tuhuma na da laifi kamar yadda ake tuhumarsa.

“Hukuncin da kotu da zartar akan ka shi ne, za’a rataye wuyanka har sai ka mutu. Ubangiji ya jikanka,” inji alkalin.

Ebenezer wanda dan asalin karamar hukumar Yagba ta Gabas ne a jihar Kogi, an gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifuka uku da suka hadar da hada baki, fashi da makami da kuma kisan kai.

Laifukan sun saba wa sashe na 6 (b), 1 (2) (a) na dokar fashi da makami, Cap R11, Vol. 14, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.

Sun kuma sabawa sashe na 316 da kuma hukunta su a karkashin sashe na 319 (1) na kundin laifuffuka, Cap C16, Dokokin eihar Ekiti, 2012.

A cewar tuhumar, Ebenezer da sauran abokan aikinsa, a ranar 29 ga watan Agusta, 2019, a Unguwar Abe Cocoa, Estate Housing Estate, Oke-Ila, Ado Ekiti, sun hada baki sun yi wa dan uwansa, Sunday Olorunleke fashin babur din Bajaj mai lambar rijista ADK 100 UJ da kudi N40,000.

A lokacin fashin, Ebenezer na dauke da wuka kuma ya kashe Sunday a ranar Lahadi.

Daya daga cikin shaidun da suka shigar da kara wanda ya bayar da shaida a gaban kotun ya ce ya je gidan wadanda ake kara ne ya sanar da shi mutuwar dan uwansa.

A cewarsa, wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa ‘yan fashi da makami ne suka kai wa dan’uwansa hari, amma ya yi zargin wanda ake zargin karya ya ke biyo bayan rashin cikakken bayani daga gareshi.

Daga baya an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Ologede.

Da ‘yan sandan suka isa wurin, an gano cewa Ebenezer ya sayar da dukkan kadarorinsa kuma yana shirin tserewa da babur din ‘dan uwansa kafin a kama shi. Daga baya ya amsa cewa shi ya kashe ‘dan uwansa.

Lauyan mai gabatar da kara, Gbemiga Adaramola, ya gabatar da shaidu biyar da suka tabbatar da laifinsa, sannan ya gabatar da bayanan wanda ake tuhuma, da hotunan marigayin, da rahoton likita da dai sauran su kamar yadda aka nuna.

Wanda ake tuhumar ya yi magana ne a kan kare kansa ta hannun lauyansa kuma bai kira shaidu ba.

Wanda ake tuhumar ya yi magana ne a kan kare kansa ta hannun lauyansa amma kuma bai kira shaidu ba.

(NAN)
Labari na baya Labari na Gaba