Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya haramtawa kungiyoyi agaji raba kayan abinci da sauran kayayyaki ga al’ummomin da gwamnati ta kara tsugunnar da su a yankunansu.

Babagana Umara Zulum
Gwamna Babagana Umara Zulum

Jaridar Peoples Gazette ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar ta sanar da dakatarwar ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Zulum.

Jawaban da ke cikin takardar wacce aka aike wa kungiyoyin jin kai ta ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya su ne;

“Gwamnatin jihar Borno, bayan tattaunawa da al’ummominta, ta yanke shawarar cewa, daga yanzu ba za a bar wata kungiyar hadin gwiwa ta raba kayan abinci ko wasu kayan agajin ba ga al’ummomin da aka sake tsugunar da su.

Gwamnatin jihar Borno ta yaba tare da gode muku bisa dukkan goyon bayan da kuke baiwa jama'a da gwamnatin jihar musamman goyon bayan da kuke baiwa mutanen da 'yan tawaye suka raba da gidajensu. 

Kamar yadda kuka sani, gwamnatin jihar Borno ta himmatu matuka wajen tallafa wa al’ummarmu domin samun karfin gwiwa da kuma tallafawa kan su don fita daga kangin talauci."

“Don haka, gwamnati ta himmatu wajen rufe duk wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri nan da Disamba 2021. Wannan ya shafi abokan hulda na gida, na kasa, da na kasashen waje. Za a ba da izinin rarraba abinci ne kawai a sansanonin IDPs a cikin yankunan da ke karbar bakuncin a yanzu.

Gwamnan ya kuma ba da umarnin cewa abokan huldar su samu izini daga gwamnati don tabbatar da daidaitawa da sanin sabbin wuraren da suke son raba abinci da abubuwan da ba na abinci ba.

Zulum ya kara da cewa, "Yayin da muke sa ran amincewa da wannan shawarar, don Allah ku yarda da godiyata bisa ga haɗin guiwarku da goyon bayanku ga jama'a da gwamnatin jihar Borno," in ji Zulum.

Labari na baya Labari na Gaba