So na iya mutuwa domin da ma shi tsuntsu ne, yau ya dira kan wannan bisa gobe waccan, amma kauna ita daram ta ke zaune wuri guda.

Maryam Ab Yola da Adam Zango
Maryam Ab Yola da Adam Zango

Fitaccen jarumi kuma mawaki na masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Adam A. Zango ya taya tsohuwar matarsa, Maryam Ab Yola murnar  zagayowar ranar haihuwarta.

Sakon da ya aike wa tsohuwar matar tasa cike suke da kauna da kuma nuna damu game da juna.

Maryam ita ce matar da Zango ya aura bayan sun kammala film din NASS, bayan aurensu ya mutu sai ta dawo Kannywood, amma yanzu ta ce ta yi fit ta fice daga Kannywood.

Yau, ranar 25 ga watan Disamba wadda ya yi daidai da ranar Kistimeti ne jarumar ke kara shekara guda a duniya, kuma ta ke bikin Birthday dinta.

“Allah ya karawa rayuwaki albarka @marryam_ab_yola Allah ya baki miji nagari!”

Jarumar ta yi godiya wa tsohon mijin nata da launin so, a sakon da ta mayar masa a fagen sharhi na hoton birthday din da ta dora.
Labari na baya Labari na Gaba