_Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce ba wani kanshin gaskiya tattare da rahoton kai harin, ya kara da cewa kawo yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaro cewa an kai hari a yankin.

_Shi ma Hakimin Dugwaba, Simon Yakubu, ya karyata tare da watsi da rahoton bogin da aka wallafa a yanar gizon.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta musanta rahoton da aka wallafa a yanar gizo cewa ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga sun kai hari mahaifar sakataren gwamnatin tarayya, SFG Boss Mustapha.

'Yan Sanda da Boss Mustapha
'Yan Sanda da Boss Mustapha

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce ba wani kanshin gaskiya tattare da rahoton da aka yada wanda ke cewa al’ummar kauyukan Dabna da Kwabre da ke yankin Dugwaba a karamar hukumar Hong sun gudun sun bar gidajensu sakamakon harin da ake zargin an kai musu.

Boss Mustapha, SGF ya fito ne daga yankin Dugwaba a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Mista Ngoruje ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) cewa, rundunar ‘yan sandan ta baza jami’anta na sirri da kuma na yaki da ta’addanci da masu garkuwa da mutane a yankin.


Ya ce kawo yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaro cewa an kai hari a yankin.

“Rundunar ta samu bayanai marasa inganci da ke cewa mutane na gudun hijira daga wasu kauyuka sakamakon haren-haren da ake zargin Boko Haram ta kai musu.

“A matsayinmu na jami’an tsaro, ba ma yin wasa da duk wani bayani ko rahoto da ya shafi rashin tsaro.

“Nan take muka tura jami’an leken asiri da na yaki da ta’addanci zuwa yankunan da ake zargi, kuma kawo yanzu babu wani rahoton kai hari a yankin ko mutanen da suka tsere daga kauyukansu,” injin Mista Nguroje.

Da aka tuntunbi Hakimin Dugwaba, Simon Yakubu, shi ma ya yi watsi da rahoton da aka wallafa a yanar gizon, ya kuma bayyana shi a matsayin “rahoton kanzon kurege kuma mai rudi”.

Mista Yakubu ya ce jama’ar kauyukan da aka ambata cikin rahoton na yanar gizo suna zaune lafiya kuma suna bikin Kirsimeti.

“Rahoton mai illa ne kuma an yi shi ne don yaudara da haifar da rudani a cikin al’ummarmu.

 “Rahoton bogin ya fito ne daga makiyan zaman lafiya da ci gaba wadanda ba sa son ganin mutane suna zaune lafiya da juna,” inji Mista Yakubu

Ya ce rahotannin da suka zo masa daga kauyukan da aka ambata a cikin labarin bogin na yanar gizon sun nuna cewa mutane na gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
Labari na baya Labari na Gaba