Rundunar 'yan sandan jihar kano ta cafke wadansu 'yan daba 13 da ta ke zarginsu da lalatawa tare da kone ofishin Barau I. Jibrin, Sanatan Kano ta Arewa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a hedikwatar rundunar da ke Jihar Kano.

Ofishin Barau Jibrin
Ofishin Barau Jibrin

"Mun samu rahoto a yau cewa 'yan daba dauke da makamai sun kai hari, sun lalata tare da kone ofishin Sanata Barau mai wakiltar Kano ta Arewa da ke kan titin Maiduguri Road," Inji shi.

Kwamishinan 'yan sanda jihar Kano, Sama'ila Shu'aibu Dikko ya umarci rundunar Operation Puff Adder da su kai daukin gaggawa wurin da lamarin ya faru, su wanzar da zaman lafiya tare da cafke masu laifin."

Ya ce cikin karsashi rundunar ta kai dauki wurin da lamarin ya faru kuma suka kama mutane 13.

A cewarsa, kayayyakin da aka kwato daga hannun 'yan daban sun hadar da makamai daban-daban, fetur galan biyu, busasshen ganyayyaki, wayar salula daya, da kuma fankoki biyu. 

Ya kuma bayyana cewa tuni an dawo da zaman lafiya kuma tuni an shawo kan lamarin.

Kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito Kwamishin 'yan sandan ya kara da cewa, "An fara bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kuliya bayan kammala binciken."
Labari na baya Labari na Gaba