Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari kan ayarin motoci sama da 10 tare da yin garkuwa da matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Yan Bindiga
Yan Bindiga

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatarwa da jaridar Daily Post aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama yayin da suka kai hari kan wasu motoci.

Hakan ya faru ne kasa da sa’o’i 12 bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Angwar Gimbiya da ke Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna ranar Talata inda suka yi awon gaba da dumbin mazauna yankin.

Ya ce akasarin wadanda masu garkuwa da mutanen ke awon gaba da su ‘yan kasuwa ne a kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Ya kuma kara da cewa, duk da rakiyar ‘yan sanda amma sai da ‘yan bindigar suka kai wa wasu motoci kimanin 18 hari.

Ya ce, "Akwai 'yan kasuwarmu kusan 70 daga garin Udawa kuma akwai wasu daga garuruwan da ke makwabtaka da Udawa a cikin ayarin motocin da aka kai wa hari a tsakanin Udawa da Buruku a kan hanyar tta Birnin Gwari"

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka tsere zuwa cikin daji sun kira ‘yan uwansu domin sanar da su halin da ake ciki.

Jami’in hula da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed ya yi alkawarin yin tsokaci kan lamarin bayan an kammala cikakken bincike.
Labari na baya Labari na Gaba