Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da sirikin Rochas Okoroca, tsohon ‘dan takarar gwamnan  jihar Imo a jam’iyyar Action Congress, mai suna Uche Nwosu.

Uche Nwosu
Uche Nwosu

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ne sanye da kakin sojoji suka yi awon gaba da Nwosu a cocin St. Peter’s Angelican Church Eziam Obire da ke karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo.

Lamarin ya faru ne yayin hidimar fitar da mahaifiyar Nwosu da ta rasu daga cocin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wadanda ake zargin ‘yan bindigar ne sun kutsa cikin cocin ne da wata motar soji suna harba harsasai a sama.

An bayyana cewa masu bashi tsaro ido suka zuba ba tare da sun yi wani katabus don taimakonsa.
Labari na baya Labari na Gaba