A kalla mutum 7 ne suka rasa rayukansu ranar lahadi bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki kasuwar Piano da ke unguwar Pinau, karamar hukumar Wase ta jihar Filato.

Yan Bindiga
Yan Bindiga

Sannan ‘yan bindigar sun raunata mutane da dama daga cikin mazauna kauyen.

Maharan sun mamaye kasuwar ne yayin da al’umma ke tsaka da saye da sayarwa a kasuwar.

A wata ruwayar, jaridar DailyPost a ranar 8 ga watan Disamba ta ruwaito cewa, mazauna wasu kauyuka sun koka sakamakon yadda‘yan bindiga suka afkawa wasu kauyukan karamar hukumar Wase, lamarin da haifar da zaman dar-dar da shakku kan motsin ‘yan bindigar.

Mazauna yankin da suka nuna fargabar sun kuma yi zargin cewa akwai ‘yan leken asiri a cikin al’ummomin yankin da su ke aiki tare da ‘yan bindigar ta hanyar kai musu bayanai game da yankin.

Shugaban matasan Wase, Shapi'i Sambo, yayin da yake tabbatar da harin na ranar lahadi da ya kai ga asarar rayuka, ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci da rashin tausayi.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigar ba su dade da mamaye kasuwar ba suka fara harbe-harbe inda suka yi barna sosai a yankin.

Haka kuma wata majiya ta bayyana cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata mazauna yankin sun ga yadda ‘yan bindiga suka tsawaita kai farmaki tare da sace mutane da dama da biyan kudin fansa.

“Yan fashin na karbar kudin fansa a miliyoyi. Wani lokaci suna karbar Naira miliyan biyu, wani lokaci kuma Naira miliyan biyar. Kwanaki ukun da suka gabata sun karbi Naira miliyan 5 kafin su sako wani mutum da suka yi awon gaba da shi kwanakin baya,” inji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, bai amsa kiran da manema labarai su ka yi masa ba dangane da lamarin..
Labari na baya Labari na Gaba