Rahotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da rasuwar mutum 38 bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyukan karamar hukumar Giwa.

'Yan Bindiga
'Yan biindiga

Da farko rundunar soji da ta ‘yan sanda sune suka bayyana cewa, mutum 20 sun rasa rayukansu a harin da ‘yan ta’addan suka kai Giwa.

Sai dai daga baya Kwamishinan Tsaro na jihar, Samuel Aruwan ya ce ‘yan bindigar sun kai hari ne a kauyukan Kauran Farawa, Marke da Riheya inda suka kashe mutum 20. Hakan na cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa, manyan motoci da kanana hadi da kayan abinci duk an kona su.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi bakin ciki da harin kana ya yi tir da shi, sannan ya yiwa al’ummar da abin ya shafa ta’aziyya.

“Gwamna Nasiru El-Rufai ya yi baƙin ciki game da harin, inda ya yiwa iyalan waɗanda abin ya shafa ta’aziya,” in ji Aruwan yayin tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Nigerian a yau lahadi.

“Bayan rahoton cewa ƴan ta’adda sun hallaka mutane 20 a karamar hukumar Giwa, Jami’an tsaro sun tabbatarwa gwamnatin Kaduna cewa adadin mutanen da a ka kashe ya ƙaru zuwa 38,” in ji Aruwan.
Labari na baya Labari na Gaba