_ Rahotanni sun ce an haifi jaririn ‘dan akuyan da siffofi irin na mutum, idanunsa, hancinsa da bakinsa kamar na mutum amma kuma kunnuwansa irin na akuya ne.

_An kuma bayyana cewa jaririn ‘dan akuyan ya rasu amma kuma kamanninsa da ‘dan adam hakan ya ba mutane da dama mamaki.

Duniya cike take da abubuwa masu matukar ban mamaki da al’ajabi, wasu za a iya bayyana su amma wasu kam sai dai a yi kurum.

Lokuta da dama a kan samun wasu tsiraru daga cikin dabbobi da su kan haifi ‘ya’ya masu kama daya sak kuma futik da mutum, da ma ai shi lamarin lillahi haka ya ke.

A wani yankin kasar Indiya mai suna Assam wani al’amari ya faru wanda mutanen yankin ba su saba gani ba inda wata akuya ta haifi jariri mai kama da mutum.

Mutanen yankin sun matukar kadu da jin labarin bayyanar wannan jaririn ‘dan akuya, nan da nan suka garzaya gidan da akuyar ta haihu domin bai wa idanunsu abinci.

Kalli hotunan akuyar da ta haifi jaririn mai kama da mutum da kuma hoton jaririn ‘dan akuyan.


Hoto: India Times

Rahotanni sun bayyana cewa jaririn ‘dan akuyan ya rasu amma kuma yanayin yadda ya ke kama  da ‘dan adam hakan ya ba mutane da dama mamaki.

Lamarin ya faru ne a kauyen Gangapur da ke mazabar Dholai Vidhan Sabha a yankin Assam.

Rahotanni sun kara da cewa an haifi jaririn ‘dan akuyan da siffofi irin na mutum, idanunsa, hancinsa da bakinsa kamar na mutum amma kuma kunnuwansa irin na akuya ne.

Kazalika rahotannin sun tabbatar da cewa jaririn ‘dan akuyan an haifeshi da kafofi biyu madadin hudu da sauran dabbobi ke da su, kamar yadda India Times ta ruwaito.

Da mutanen ƙauyen suka ji labarin wannan halitta mai kama da mutum , sai suka taru don ganin gawar dabbar. Lokacin da suka ga yaron ‘dan akuyan da aka haifa, sun kasa gaskata idanunsu cewa akwai wani abu mai ban mamaki irin wannan.
Labari na baya Labari na Gaba