Amina Uba Hassan, tsohuwar matar fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango, ta dawo masana'antar a matsayin cikakkiyar jaruma.

Jaruma Amina 

Amina wacce aka fi sani da Maman Haidar ta zama jaruma a Kannywood a farkon shekarar 2000 amma sai ta ajiye sana'arta ta fim ta auri Adam Zango a shekarar 2007.

Ta haifi da namiji a shekarar 2008 sai dai kuma auren na ta ita da Adam A. Zango bai yi wani dogon zamani ba, domin bayan wata biyar saki ya shiga tsakaninsu.

To, bayan igiyar aurenta ta katse, jarumar ta ci gaba da daina fitowa a finafinai, sai dai ta sake fitowa a wani shiri na gidan talabijin mai suna ‘Gidan Danja’ wanda kamfanin 2Effects ya shirya a kwanakin baya.

Jarumar, haifaffiyar jihar Kaduna ta ce ta dawo masana'antar da karsashinta fiye da lokacin da ta bar ta, kuma wannan lokacin samaniyar Allah ce iyakarta.

"Yana da matukar wahala a matsayin uwa wacce aka sake ta na dawo masana'antar cikin nasara bayan shafe fiye da shekaru 10 ba tare da bayyanata ba, dole sai da karfin hali da kuma shawarwari don samun damar yanke shawara.

"A bayyane yake cewa wasan kwaikwayo shine abin da nake son yi kuma wasan kwaikwayo shine abin da zan yi,” inji ta.

Masoya sun yi ta yabawa rawar da ta taka a shirin da ake yadawa a tashar Arewa24.
Labari na baya Labari na Gaba