Allah dai kam ya wadaran na ka ya lalace. Hukumar NSCDC ta kama wani tsoho dan shekara 75 bisa zargin yi wa yarsa ta cikinsa mai shekara 17 fyade fiye da sau hudu.

Lamarin dai ya faru ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, budurwar da tsohon mai suna Rojaiye Balogun ya yi wa fyaden ta roki 'yan jarida da su sakaya sunanta.

Fyade
Fyade | Hoto: Dailytrust.com

Yayin gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar hukumar NSCDC da ke Abeokuta, kwamandan hukumar, Kolawole Taiwo, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Imomo, karamar hukumar Ijebu Ode ta jihar, ranar Laraba.

Taiwo ya bayyana cewa, 'yan uwan wanda abin ya shafa sune suka kai rahoton fyaden ga sashen yaki da fataucin bil'adama da hijira ba bisa ka'ida ba.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana lalata da yar ta sa, inda ya ce sharrin shaidan ne.

Shugaban NSCDCn ya kara da cewa, za a binciki lamarin kuma in dai aka samu wanda ake zargin da aika laifin, to tabbas za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Ya kuma koka da yadda ake samun karuwar lalata tsakanin 'yan uwa na jini da cin zarafin ‘ya’ya mata a cikin al’umma, inda ya ce a bisa dokar kare hakkin yara, iyaye suna da hakkin karen 'ya'yansu. Kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito

Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya yi ikirarin yarinyar ba yarsa ce ta cikinsa ba, sannan ya yi lalata da ita sau daya tak a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya.

Amma, wacce aka ma fyaden ta musanta ikirarin na mahaifinta, inda ta ce sau hudu yana yi mata gyade. 

Ta kuma kara da cewa, tsohon karya ya yi cewa ita ba yarsa ba ce ta cikinsa." 

Ta ce a karo na karshe wanda ake zargin, ya yi mata alkawarin zai ba ta Naira 1,000 domin ta barshi ya kwana da ita, "Ni kuma na ki, amma ya haka ya min fyaden karfe da yaji."

Ta ce, ta sha kai rahoton lamarin ga mahaifiyarta amma ba ta yarda da ita ba.

Kazalika ta kara da cewa, wani kawunta ne ya kai ta ofishin hukumar NSCDC ta kai karar mahaifin nata.
Labari na baya Labari na Gaba