Takardar Bello Turji
Takardaar Neman Sulhun Bello Turji


ASSALAMU ALAIKUM, WARAHMATULLAHI, WABARAKATUHU, BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM. 

Daga Muhammadu Bello Turji, fakai, innadinin indalahi al-islam, al-muslims ahlul-muslims. 

Muna godiya ga Allah (S.W.T) daya nuna mana wannan lokaci, ga sako nan zuwa ga Masarautar Shinkafi, zuwa ga mai girma Gwamnan jihar Zamfara barden kasar Hausa, Alh. Muhammadu Bellow Matawallen Maradun, zuwa ga Shugaban kasa mai girma General Muhammadu Buhari (R.T.A). Wanda ya rubuto wannan takarda shine: Muhammadu Bello Turji Kacalla wanda ku keji. 

Bayan haka, ya mai girma Emiya na Shinkafi, da mai girma Gwamnan jahar Zamfara, ku dubi Allah (S.W.T) da darajar Annabi Muhammadu (S.A.W). Makasudin wannan takarda shine kamar haka:- 

Na daya: shine kashe-kashen da ake yi na al’umma wadanda basu ji, basu gani ba, ya kai karshe, domin ‘yan bindiga su kashe, ‘yan sa kai su kashe, kuma jami’an tsaro su kashe, da kuma daukar mutane domin karbar kudin fansa, to Insha Allahu (S.W.T) za’a kai karshenshi da yardar ubangiji Allah, matukar gwamnati za ta soke kungiyar ‘yan sa kai, Insha Allahu za mu aje makamai duka. Matukar aka kawar da kabilanci da ake nuna mana, da son rai, mu dawo mu zauna abu daya kamar yadda muke da can, uwa daya uba daya, mu yafe ma juna bisa ga kaddarar Allah. 

Abu Na biyu: Ya mai girma Emiya, da mai girma Gwamna, muna bukatar zama da sarakunan kasar nan tamu da kuma manyan malaman musulunci na kasarmu baki daya, idan haka ta samu ni Muhammadu Bello Turji Kacalla na yi alkawali har ga Allah zan karbi duk bindigogin da ake ta’addanci da su in hannuntasu ga hukumar Najeriya, matukar gwamnati za tayi mana adalaci da kuma kulawa damu, da bamu duk hakkokinmu kamar yadda ake kula da sauran jama’ar kasa, kuma a bar cin zarafinmu. 

Sai Abu na Ukku, Shine: Ya maigirma Emiya da maigirma Gwamnan Zamfara mai adalci, barden kasar Hausa, ina tabbatar ma cewa mu ba ma fada da gwamnati, kuma ba mulki muke nema ba, kuma ba wata kungiya muke son kafawa ba, a’a wallahi abubuwan da ake wa fulani a kasar nan na cin zarafinmu da nuna mana banbanci ko a cikin kasuwanni da kuma cikin garuruwa shi ya haddasa wadannan abubuwa na rashin zaman lafiya. 

Abu na Hudu, ya mai girma Emiya kasanni ba barawo bane, don haka na rubuto wannan takarda tsakanina da Allah, ba da wata yaudara ba, kuma kada ku yaudaremu, kuma kada ku mana zagon kasa, muyi dan Allah kuma dan kasarmu ta zauna lafiya kamar yadda muke can da. Kowa ya tsaya wurinshi mu bar jami’an tsaro su yi aikinsu yadda suka saba a hukunta mai laifi bada nuna wani bangaranci ba, in Allah ya yarda ba za’a sake ganin bindiga sai ga jami’an tsaro kamar yadda aka saba gani. 

Sai abu na karshe shine, wannan zama da za’ayi idan har za’ayi shi to don Allah, a hada sarakuna da manyan malaman addinin musulunci na kasar nan gaba daya, kuma muna bukatar ganin Sheikh Ahmad Abubakar Gumi wajen zaman da za’ayi na kaiwa karshen wannan ta’addancin, domin shi muka sani domin ya taba kawo mana ziyara; kuma yayi mana wa’azi, kuma yanzu munga amfanin wa’azin, don haka muna son kasarmu ta zauna lafiya da yarda Allah (S.W.T). 

HAZA WASSALAM, ALLAH SHI BAMU IKON RIKE ALKAWALI. 

DAGA MUHAMMADU BELLO TURJI KACALLA FAKAI.

Ga takardar nan cikin hotuna a rubuce a hoto an yi scanning dinta.

Labari na baya Labari na Gaba