Labaran mutuwar jaruman fina-finan hausa na masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood har sun zama ababen kurna muhawara a shafukan sada zumunta, sai ka ji ance kwatsam wane ko wance ta rasu, alhali kuwa karya ne.

Jarumi Lawan Ahmad
Lawan Ahmad | Hoto: Instagram.com

Ita dai mutuwa bai kamata a rinka yin karyarta ba, domin ba karamin al’amari ba ne ace wane ko wance ta mutu.

Sai dai, a masana’antar kannywood jaruman masana’antar ba su dauki hakan a matsayin wani babban abu ba, wannan ya sa su kansu suke yada labarin mutuwar abokan aikinsu ba tare da sun tace tsagwaron gaskiyar labarin ba.

Wasu lokutan kuma ba su suke yadawar ba, lala, marubutan yanar gizo (bloggers) su ne suke wallafa irin wadannan labaran na karya, hmm abun sai a yi kurum.

Tsakanin jiya-da-yau mashahurin mawakin Kwankwasiyya, Tijjani Gandu ya fitar da labarin rasuwar abokin sana’arsa mai shirya shirin Izzar So, Jarumi Lawan Ahmad.

Tijjanin ya bayyana cewa ya yi tafiya zuwa Kaduna, yana dawowa sai ya tarar an kawo masa labarin rasuwar Lawan Ahmad ofishinsa bayan ya yi tafiya, kana ya ce amininsa ne ya tabbatar masa da hakan.

Har kanensa ya kira don ya ji ko da gaske ne? Sai ya tabbatar masa eh tabbas sako dai an turo masa.

Daga nan sai shi Tijjanin ya kira lambar Lawan ya fi sau 50 ba’a daga ba, hakan ya tabbatar masa a ransa eh Lawan Ahmad din ya rasu.

Lawan Ahmad na Raye bai Mutu ba

To, a wani faifan bidiyo da Tijjanin ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya yi amai ya lashe sannan ya ce Lawan na raye bai mutu ba.

Kazalika, ya kuma baiwa dukkanin daukacin al’umma hakuri domin shi ne ya fara fitar da labarin mutuwar Lawan Ahmad din.

Mai son kallon cikakken bidiyon sai ya latsa nan

Yaki da Labaran Karya a Kannywood

A baya-bayan nan jarumai da dama sun sha daure mutanen da suka wallafa labaran karya a kansu, musamman jarumai mata.

Sai dai har yanzu ba mu ji labarin wani mataki da masana’antar ta ke shirin dauka ba a kan duk masu yada labaran karya game da masana’antar da jarumanta.

To, ko ma dai menene, za mu so masana’antar kannywood ta fara tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.
Labari na baya Labari na Gaba