Sanatan Jigawa ta arewa maso gabas, Barista Ibrahim Hassan Hadejia ya baiwa wani dalibi Gurgu na Sikandaren jeka ka dawo ta Mallam Madori mai suna Hassan Musa keken guragu  domin zuwa makaranta.

Sanata Ibrahim Hassan Hadejia
Sanata Ibrahim Hassan Hadejia

Sanata Ibrahim Hassan ya bada gudunmawar ne sakamakon ganin fefen video yaron a shafin face book da yake neman taimako.Yaron ya kasance yana zuwa makaranta da rarrafe wani lokacin ma in yayi dace akan rage masa hanya a tafiya ko a dawowa. 

Kalli hoton gurgun yayin da ya ke amsar kyautar keken:

Shugaban makarantar shine ya jagoranci bikin baiwa yaron keken guragun. Kamar yadda Jigawa Radio ta ruwaito.

Labari na baya Labari na Gaba