Jamhuriyar Nijar, Benin da Togo ba su biya kudin wutar lantarkin da Najerita ta basu ba a zango na biyu a shekarar 2021, inji hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya.

NERC

NERC ta bayyana cewa kamfanonin samar da wutar lantarki na kasashen uku hadi da wasu kwastomominsu na musamman sun samu tsurar kudi Naira miliyan 770 daga hannun kamfanin Trading Bulk Electricity da kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya.

Sai dai kuma ta yi nuni da cewa, Najeriya ba ta samu wani kaso ba a matsayin kudin wuta daga kasashen da kuma sauran kwastomominsu na musamman a lokacin.

Kamfanonin da ba su biya kudin wutar lantarkin da Najeriya ta samar musu ba a zango na biyu a shekarar 2021 sune;
  1. Kamfanin Lantarki na jamhuriyar Nijar, Societe Nigerienne d'electricite – NIGELEC
  2. Kamfanin lantarki na Jamhuriyar Benin, Societe Beninoise d'Energie Electrique - SBEE,
  3. Sai kuma kamfanin lantarki na Jamhuriyar Togo, Compagnie Energie Electrique du Togo- CEET, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Labari na baya Labari na Gaba