Kimanin mutane 30 ne aka tabbatar da sun kamu da zazzabin Lassa a kananan hukumomi shida na jihar Bauchi.

An samu yawaitar cutar ne sakamakon girbin kayan amfanin gona da aka yi a bana.

Lassa Fever
Lassa Fever

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na Jihar, Dokta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ‘yan jarida kan halin da cutar ke ciki, wanda aka gudanar a cibiyar bayar da agajin gaggawa (EOC) da ke Bauchi.

Dr Mohammed ya ce kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Bauchi, Bogoro, Ganjuwa, Kirfi, Tafawa Balewa da Toro. Kamar yadda Radio Nigeria Kaduna ya ruwaito.

Ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Disamba na wannan shekarar, jihar ta samu mutane 135 da ake zargin sun kamu da cutar, daga cikinsu an gwada mutane 136 sannan an tabbatar da mutuwarmutane takwas.

Dokta Mohammed ya ce gwamnatin jihar na daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsaron lafiyar jama’a, yana mai jaddada cewa hukumar na jiran sa hannun gwamnan jihar domin sayo karin magunguna da alluran da za a magance cutar.

Shugaban ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika kula da tsaftar mutum da ta muhalli, domin dakile yaduwar zazzabin Lassa da sauran cututtuka masu yaduwa.

Labari na baya Labari na Gaba