Yanzu-yanzu muka samu labarin rasuwar fitacciyar mai koyar da salon jima'in nan ta Arewacin Najeriya a Youtube, Munirat Haruna Abdussalam wadda aka fi sani da Muneerat Abdussalam ko kuma Uwar Lumancy.

Muneerat Abdussalam
Muneerat Abdussalam

Kamar yadda ahalin mamaciyar suka wallafa a shafinta na Facebook, mamaciyar mutuwa ta mata fab daya ne, bi ma'ana mutuwar bazata

Muneerat Uwar Lumancy ta rigamu gidan gaskiya tana da shekaru 33 a duniya.

Sai dai har yanzu mabiyan ita Muneerat Abdussalam sun yi fau-fau sun ce sam ba su yarda da mutuwar tata ba, domin an sha su sun warke.

A baya an taba samun wacce ta fitar da labarin rasuwarta ta asusunta na facebook, wadda hakan ya yamutsa hazo a shafukan sada zumunta, daga baya aka gane ashe karya ta ke yi.

Wannan shi yasa wasu mabiyan na Uwar Lumancy suka ce su basu yarda ta mutu ba. Ga dai irin maganganun da suke yi

Usman Janti cewa ya yi:

Mansir Munir Sinifos shi kuwa kun ji abinda ya ce:


Shi kuwa Atsaktiya Raphael Musa cewa ya yi:


Da wannan muka kawo karshen rahoton, in har da gaske Uwar Lumancy ta rasu, muna fatan mai duka ya amshi tubanta, ya gafarta mata.
Labari na baya Labari na Gaba