_ Malaman sun yi wannan kira ne a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Nigeria Kaduna a Gusau

_Sheik Umar Kanoma ya yi kira da a gudanar da addu’o’in kawo karshen ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da suka shafi jihar

_Shugabar kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar Zamfara, Lami Mangze ta yi kira da a zauna lafiya da kowa da kowa

A yayin da shekarar 2021 ta zo karshe, malaman addini a jihar Zamfara sun yi kira da a gudanar da addu’o’i na musamman da kuma yawaita addu’o’i domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma kasa baki daya.

Taswirar Zamfara
Taswirar Zamfara

Malaman addinin sun yi wannan kiran ne a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya Kaduna a Gusau babban birnin jihar.

Da yake jawabi kwamishinan harkokin addini na jihar Dr Muhammad Tukur Sani Jangebe ya bayyana shekarar 2021 a matsayin shekara mai cike da masifu dake bukatar tuba gaba daya zuwa ga Allah madaukakin sarki domin kariya daga sake ganin irin wannan bala’i.


Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su mika wuya su mika kansu ga  Allah da koyarwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama tare da kaucewa duk wani abu da zai iya bata sunan su da na addini.

Hakazalika, a nasa gudunmuwar, Sheik Umar Kanoma ya yi kira da a gudanar da addu’o’in kawo karshen ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da suka shafi jihar da yanki da ma kasa baki daya.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su rika tsoron Allah a cikin harkokinsu na yau da kullum, su rubanya ibada, da neman gafarar Allah Madaukakin Sarki.

Shima da yake jawabi, shugabar kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar Zamfara, Lami Mangze ta yi kira da a zauna lafiya da kowa da kowa da kuma yafewa duk wanda ya bata maka rai.

A wani labarin kuma, Bishop Christ Cathedral, Cocin Anglican Communion Church, John Danbita ya kuma yi kira ga mabiya addinin Kirista da su guji duk wani abu na kawo rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara da kasa baki daya.

Hakazalika, Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello wanda ya yi magana ta bakin Chiroman Gusau, Alhaji Mainasara Bello, ya bukaci jama’a da su zauna lafiya a ko da yaushe tare da kyautata al’adun hadin kai, a hada kai da taimakon juna.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar kalubalen tsaro tsawon shekaru goma sha biyu da kuma tabarbarewar siyasa da tattalin arziki.
Labari na baya Labari na Gaba