Majalisar dokokin Jihar Kano ta zartar da wani kudiri na neman gwamnatin jihar ta gina hanyar da ta hada Malamai Makarantar Tsamiya Babba zuwa Gidan Kwano da Mariri a kan titin Maiduguri.

Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnn Kano, Ganduje

Kananan hukumomin da wannan titin zai hada sun hadar da karamar hukumar Gezawa da karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan amincewa da wani kudirin hadin gwiwa da Honorable Isiyaku Danja (Gezawa- PDP) da Honorable Mudassir Zawaciki (Kumbotso- PDP) suka gabatar a zaman majalisar a ranar Litinin.

Da yake gabatar da kudirin, Honorable Danja ya bayyana cewa gina titin zai taimaka wajen magance mafi yawan kalubalen da al’ummar yankin ke fuskanta.

“Hanyar tana bukatar kulawar gwamnati bisa la’akari da muhimmancinta ga ci gaban al’umma, musamman a fannin tattalin arziki, ilimi, tsaro da samar da kiwon lafiya ga jama’a.

"Yana da matukar muhimmanci a gabatar da kudirin a gaban majalisa tare da yin fatan gwamnati ta gina hanyar," in ji Mista Danja.

Bayan haka ne majalisar ta amince da kudirin tare da yin kira ga gwamnati da ta gina hanyar.

Labari na baya Labari na Gaba