_Mohammed Shehu ya koma tsagin da Shekarau ke jagoranta, ya ce saboda rashin kyakkyawan shugabancin Abdullahi Abbas ya koma daya tsagin

_Ya kuma kuduri aniyar cewa shi da magoya bayansa za su-yi-ruwa-su-yi tsaki don tabbatuwar nasarar Barau jibrin a zaben 2023

Mai bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin jihar Kano, Mohammed Sheku ya koma tsagin da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta a jam’iyyar APC a jihar.

Ganduje da Mohammed Shehu
Ganduje da Mohammed Shehu

Da yake jawabi ga dubban magoya bayan jam’iyyar APC a karshen mako a Kano, Mista Shehu ya ce ya yanke shawarar koma wa tsagin Shekarau tare da dubban magoya bayansa ne saboda rashin kyakkyawan shugaban da Abdullahi Abbas ke gwadawa a jam’iyyar.

Hotunan wurin taron jam'iyyar ta APC da kuma magoya bayan Mohammed Shehu:

Mohammed Shehu da Magoya Bayansa

Taron Magoya bayan Mohammed Shehu

Mista Shehu ya ce magoya bayansa sun kuduri aniyar bada tasu gudunmawar domin tabbatar da nasarar Barau Jibrin Maliya a takararsa ta Gwamna.

“Duk da cewa mafi yawan al’ummar karamar hukumar Nassarawa suna tare da mu, amma shugabannin da Abdullahi Abbas ke jagoranta sun rufe ido kan wannan lamari, suna goyon bayan wasu da ba sa goyon bayan talakawa.

“Bari in gaya muku cewa ba mu kadai muke cikin wannan tafiya ba. Masu ba da shawara da manyan ’yan siyasa sun fi karkata ga sahihancin shugabancin Danzago a APC, kuma muna gida cike da burin ganin Sanata Barau Jibrin ya ci nasara.

 “Sanata Barau Jibrin mutum ne mai gaskiya kuma amintacce wanda kowa ya yarda da shi. Ba kakaba wa mutanen Kano shi ake son yi ba, sai dai su kansu mutanen ne suke son dora shi,” inji shi.

Tun bayan da kotu ta ayyana Haruna Danzago a matsayin sahihin shugaban jam’iyyar APC a Kano wasu da dama daga cikin magoya bayan gwamnan suka kafa sauya sheka zuwa tsagin Shekarau.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka daga tsagin Ganduje kwanan nan akwai tsohon mataimakinsa, Hafiz Abubakar da kuma daya daga cikin makusantan sa, Murtala Zainawa.
Labari na baya Labari na Gaba