Kungiyar Arewa Legend da ke jihar Bauchi ta baiwa jaruman cikin shirin nan mai dogon zango (Labarina) kyautar gwarzon n jarumai a shekarar 2021.

Duba da irin yadda jarumi Lukman na cikin shirin Labarina ya matukar shiga damuwa a cikin shirin ya kuma nuna kawa-zuci sosai, hakan bashi damar lashe kyautar “Best Emotional Actor of The Year”.

Lukman, Adama da Umar
Lukman, Adama da Umar

Lukman ya nuna jin dadinsa kwarai da gaske kana ya kuma gode wa Malam Aminu Saira da ya bashi wannan role din.

Shi kuma Umar, abokin Mahmud a cikin shirin ya samu nasarar lashe kyautar “Best Talented Actor of the Year” sakamakon yadda ya nuna hikima da basira a cikin shirin.

Ita ma Adama wadda aka fi sani da Adamar Kamaye ta samu nasara lashe daya daga cikin kyautar ta jarumai gwarazan shekarar 2021 a cikin shirin labarina.

Kar dai na cikaku da surutu, ga hotunan yadda abin ya kaya nan kowa ya gani:

Kai da ganin hotunan nan ka san jaruman sun matukar jin dadin irin wannan karramawa da kungiyar Arewa Legend da ke jihar Buachi ta yi musu.


Labari na baya Labari na Gaba