Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta ce jam’ianta sun kama wasu magunguna da aka shigo da su daga kasashen waje da suka hada da magungunan kara kuzarin jima’i da sauran kayayyaki a jihar Katsina da kudinsu ya kai ₦110.890m.

Useni A. Aliyu
Mai Gudanarwa, Useni A. Aliyu

Useni Aliyu, mai gudanarwa a Strike Force Zone ‘B’, DC, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Katsina yayin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce an kama su ne daga ranar 2 ga watan Oktoba zuwa  yau.

Ya kuma kara da cewa hukumar ta kama kwalaye 52 na magunguna daban-daban masu dauke da jabun lambobin NAFDAC da kudinsu ya kai ₦6.102m da kuma wani babu da kudinsa ya kai ₦60,000.
 
“A tsawon lokacin da muke bitar, mun kuma iya kama buhunan shinkafa ta kasar waje 450 mai nauyin kilogiram 50 wanda kudinsu ya kai ₦10.890m.
 
“Mun kuma kama wasu buhunan shinkafa guda 100 kowannensu mai nauyin kilogiram 25 da kudinsu ya kai ₦1.210m, katan 300 na spaghetti ta kasashen waje da darajarsu ta kai ₦1.080m.

“Jami’an mu sun kuma yi nasarar kama katan 790 na sabulun kasashen waje wanda kudinsu ya kai ₦91,008, 000 wadanda aka boye a cikin fakitin noodle,” inji shi.
 
A cewa Mista Aliyu, wannan nasarar na daga cikin kokarin da suke na yaki da fasa kwauri a yankin domin cimma manufarsu ta dakile fasa kwauri baki daya.

“Dakile ayyukan fasa kwauri aiki ne na cigaba, kuma yunkin ba zai gaza ba a kokarinsu na tabbatar dakile fasa kwauri ta hanyar toshe duk wani lungu da sako,” inji shi.

Ya bayyana cewa ci gaba da dakile shigo da shinkafar kasashen waje zai taimka wajen karfafa gwiwar manonman cikin gida da su kara zage damtse wajen noma don tallafawa tattalin arzikin kasar.

Mista Aliyu ya ce, a lokacin da ake binciken, an kama mutane uku da ake zargin an kuma bayar da belinsu, yanzu haka ana jiran kammala bincike.
Labari na baya Labari na Gaba