Wata babbar kotun jihar Kano ta hana gwamnatin jihar gina shaguna a tsakiyar titin kasuwar Kofar Wambai da ke karamar hukumar Manucipal.

A baya bayan nan ‘yan kasuwar Kofar Wambai suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da gina shagunan a lokacin da gwamnati ta fara aza harsashin ginin.

Masu zanga-zanga a Kasuwar Kofar Wambai
Masu zanga-zanga a Kasuwar Kofar Wambai

‘Yan kasuwar sun ce aikin zai yi illaci harkokin kasuwanci su, domin tsakiyar titin da aka fara ginin a kansa shi ne falali mafi girma a kasuwar inda ake ajiye ababen hawa don lodin kayayyakin da za a kai wasu wuraren a kasar nan.

A kokarin ‘yan kasuwar na dakatar da aikin, sun maka gwamnatin jihar Kano a kotu.

 Bayan sauraron karar da ‘yan kasuwa suka shigar a ranar Juma’a, mai shari’a Aisha Ya’u ta bayar da umarnin hana gwamnatin jihar ci gaba da gudanar da aikin sai an saurari karar da kuma yanke hukunci. 
 
Ta ba da umarnin cewa bangarorin biyu su kiyaye matsayinsu a filin da ake takaddama a kai.

“An ba da umarnin cewa bangarorin za su dakatar da duk wani aiki kan filin da ake takaddama a kai kuma su ci gaba jiran lokacin da za a cigaba da sauraren karar da kuma yanke hukunci bayan sanarwar.

"An daga shari'ar zuwa ranar 24/01/2022," in ji kotun.

Kotun ta yi la’akari da hukuncin ne bayan wani motion da lauyan ‘yan kasuwar ya kawo a ranar 17 Disamba 2021 tare da rakiyar rantsuwa.

Lauyan ‘yan kasuwar, Sadiq Abdullahi, ya ce tuni gwamnati ta aza harsashin ginin shaguna a kan hanyar shiga kasuwar.

 ‘Yan kasuwar karkashin jagorancin Ibrahim Yakasai sun garzaya kotu ne a ranar 22 ga watan Disamba domin dakatar da shirin gwamnati na gina karin shaguna a kasuwar da ke cike da cunkoso.
 
Wani dan kasuwa a kasuwar, Anas Bala, ya shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa bai dace a gina shaguna a kan titin ba, inda ake shiga da fitar da kayayyaki kuma motocin kashe gobara suna shiga kasuwar lokacin gaggawa.
Labari na baya Labari na Gaba