Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan kisan gillar da aka yi wa maoma 45 tare da raunata wasu da dama a Jihar Nasarawa.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

'Yan bindiga ne suka kashe manoma 45 tare da jikkata wasu a kananan hukumomin Lafia, Obi da Awe da ke jihar.

Shugaba Buhari ya ce al'ummar kasar baki daya sun tausayawa iyalan wadanda abin ya shafa. Kamar yadda Garba Shehu ya bayyana.

"Ina tabbatar wa jama'a da gaske cewa wannan gwamnati tana yin iya kokarinta wajen ganin ta kare lafiyar jama'a kuma lallai za ta kamo wadanda suka aikata wannan ta'asa ta rashin hankali da dabbanci tare da gurfanar da su a gaban kuliya," inji shi.

 Ya kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar, ya kuma nuna jin dadinsa da yadda gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa kan lamarin.

Labari na baya Labari na Gaba