_ Hajiya Yabawa Kolo ta ce ‘yan gudun hijirar da aka sake tsugunar da su sun fito ne daga sansanoni shida na Bakasi, MOGOLIS, NYSC, Farm Centre, Muna Dayalti da Haruna Alana.

_ Yabawa Kolo kuma ta bayyana cewa hukumar ta tallafawa yara sama da dari da ‘yan tada kayar bayan suka maida marayu domin samun ingantaccen ilimi. 

Gwamnatin jihar Borno ta sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kimanin dubu dari bakwai zuwa garuruwansu na iyaye da kakanni. 

Gov Zulum da 'Yan Gudun Hijira
Gov Zulum da 'Yan Gudun Hijira

Darakta Janar ta Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta SEMA, Hajiya Yabawa Kolo ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Maiduguri. 

Yabawa Kolo ta ce ‘yan gudun hijirar da aka sake tsugunar da su sun fito ne daga sansanoni shida na Bakasi, MOGOLIS, NYSC, Farm Centre, Muna Dayalti da Haruna Alana.


Ta yi bayanin cewa nan ba da jimawa ba za a mayar da ‘yan gudun hijirar da ke sansanin Village Teachers da kuma sansanin Staduim zuwa garuruwansu bayan kammalar dukkan ka’idoji. 

Darakta Janar din ta jaddada kudirin gwamnatin jihar na rufe dukkanin sansanonin jami’ai 28 da ke Maiduguri nan da 31 ga watan nan.

A cewarta, ana gudanar da aikin dawowa da ‘yan gudun hijirar ne bisa ka'idojin kasa da kasa, wato da son rai kuma cikin mutunci. Kamar yadda Radio Nigeria Kaduna ta ruwaito.

Hajiya Yabawa Kolo ta bayyana cewa hukumar ta tallafawa yara sama da dari da ‘yan tada kayar bayan suka maida marayu domin samun ingantaccen ilimi. 

Ta yi alƙawarin ƙarfafa dawowar 'yan gudun hijira a cikin shekara ta 2022 sannan ta kuma fara shirye-shiryen kwantar da tarzoma ga IDPs masu dogaro da kai.
Labari na baya Labari na Gaba