_ Ma'ikatar Ayyuka da Sufuri ta gargadi mutanen jihar jigawa kan gina kabarin mai tatsine da giciye itatuwa kan hanyoyin jihar

_Mai magana da yawun ma'aikatar ne ya aike da wannan gargadi

_Kuma ya bayyana cewa gwamnati za ta hukunta duk wanda aka kama da gina kabarin mai tatsine ko shinge kan hanyoyin jihar.


Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga yanzu ta haramta gina kabarin mai tatsine da kuma kafa shinge a kan dukkanin hanyoyin jihar, hakan ya fito ne daga Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta jihar.

Badaru Abubakar
Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar

Haka kuma ma’aikatar ayyuka da sufurin ta haramta giciye itatuwa da wasu mazauna jihar suke yi domin rage wa motoci gudu idan sun shigo gari.

Domin giciye itatuwan na haifar da asarar rayuka ne da dukiyoyin al’uma kamar yadda kamar yadda ma’aikatar ta shaida wa Gidan Rediyon Jigawa.


Bisa wannan dalili gwamnatin jihar jigawa ta sha alwashin cire dukkanin shingayen da aka kafa a kan titunan jihar ba bisa ka’ida ba.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta jihar, Usman Gumel shi ya aike da wannan gargadi ga al’ummar jihar.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta hukunta duk wanda aka kama da kafa shinge a kan hanyar wucewar motoci ta jihar.
Labari na baya Labari na Gaba