Kididdigar fasfo din duniya ta shekarar 2021 ta bayyana cewa masu rike da fasfo din Najeriya na iya tafiya kasashe guda 26 ba tare da biza ba.
Fasfon Najeriya
Fasfon Najeriya | Hoto: Getty Images

Sannan za kuma su iya tafiya kasashe 19 wadanda da zarar sun isa kasar sai su yanki biza, hakan ya cika jadawalin kasashe 45 da ‘yan Najeriya za su iya zuwa.

Haka kuma a cikin kundin kididdigar, Najeriya ta zo ta 103 cikin kasashe 106 da suke da nagartattun fasfon tafiye-tafiye a duniya.

Kasashen Afirka:

 1. Benin
 2. Burkina Faso
 3. Cameroon
 4. Cape Varde Islands
 5. Chad
 6. Cote d’Ivoire (Ivory Coast)
 7. Gambia
 8. Ghana
 9. Guinea-Bissau
 10. Liberia
 11. Mali
 12. Niger
 13. Senegal
 14. Sierra Leone
 15. Togo

Kasashen Carribean

 1. Barbados
 2. Dominicia
 3. Haiti
 4. Montserrat
 5. St. Kitts and Nevis

Kasashen Oceania

 1. Cook Islands
 2. Fiji
 3. Micronesia
 4. Niue
 5. Vanuatu
Ƙididdigar Henley Passport Index ce ta buga rahoton, wadda ta bayyana kanta a matsayin ta zahiri kuma mai ikon auna duk fasfo din duniya gwargwadon adadin wuraren da mai riƙe da shi zai iya tafiya zuwa ba tare da biza ba. 

Kamar yadda majiyar Legit.ng ta tattaro, an gudanar da wannan kididdigar ne a kan wasu bayanai na musamman daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA).
Labari na baya Labari na Gaba