Jagoran juyin mulkin da aka yi na 2008 a kasar Guinea, Moussa Dadis Camara, ya koma kasar a ranar Laraba, 12 ga watan Disamba, 2021, bayan ya kwashe fiye da shekaru goma yana gudun hijira.

Moussa Dadis Camara
Moussa Dadis Camara

Ya bayyana cewa zai amshi hukuncin da za a yanke masa kan laifukan da aka aikata yayin da ya ke mulki.

Magoya bayan sojan sun tarbe shi a filin tashi da saukar jiragen sama na Conakry babban birnin kasar suna raye-raye da rera waka sanye da riga mai dauke da tambarin fuskarsa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce Camara, shi ne sojan da ya jagoranci shekara mai cike da hargitsi a kasar Afirka ta Yamma a shekarar 2009.

A watan Satumbar shekarar 2009 ne sojojin da ke karkarshin Camara suka bude buta kan taron ‘yan adawa da suka taru a filin wasa, a wurin kuma aka yi wa fiye da mata 100 fyade.

Masu fafutuka sun yi ta neman a yi musu adalci kan kisan kiyashi da fyaden da aka yi, amma a shekarar 2017 ne aka kawo karshen binciken lamarin ba tare da shari’a ta yi hukunci ba.

“A shirye nake na mika kaina gaban kotu saboda babu wanda ya fi karfin doka,” Camara ya bayyana hakan ne wa manema labarai a Burkina Faso, inda ya ke gudun hijira.

Ya ce yana son a yi shari’a kan kisan kiyashin da aka yi a filin wasan saboda hakan zai kawo sa’ida ga iyalan wadanda abin ya shafa.

An nada Camara a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soji da ta kwace mulki a watan Disambar 2008 bayan mutuwar shugaba Lansana Conte da ya dade kan mulki.

Sai dai harin kwanton baunar da daya daga cikin abokan aikinsa ya kai masa har ya yi nasarar harbinshi a ka ya tilastawa Camara yin gudun hijira.

Kasar Guinea ta sake fuskantar wani juyin mulki a watan Satumban bana, kuma gwamnatin da ke mulki a yanzu ta amince da ziyarar Camara bisa dalilan jin kai.

Sai dai kuma shugabannin na yanzu sun ce sun shirya gudanar da shari’a kan kisan kiyashin da aka yi a shekarar 2009..
Labari na baya Labari na Gaba